2 Yuli 2025 - 09:48
Source: ABNA24
Manjo Janar Safawi: Ba Za Mu Bar Jinanan Shahidanmu Ba, Za Mu Faruci Amurka Da Gwamnatin ‘Yan Mamaya Har Zuwa Karshe.

Manjo Janar Safawi ya ce: "Kowa ya tabbatar da cewa karfin duniyar musulmi zai tai galaba a kan kasashen yammacin duniya, wajibi ne yahudawan sahyoniya da Amurka su gane cewa al'ummar Iran ba za su bar su su ayyukansu ba, ba za mu yi watsi da jinanan shahidanmu ba, kuma za mu bi su har zuwa karshe.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul bayt As ABNA ya habarta cewa: babban mai ba da shawara kuma mataimaki na musamman ga babban kwamandan sojojin kasar Manjo Janar Sayyid Yahya Safawi ya bayyana cewa, idan makiya suka sake yin wani kuskure, to dukkanin wurare da sansanonin su za su fuskanci mummunan hare-hare, kuma za su fuskanci hatsari mai tsanani, karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci.

A gefen taron tunawa da Laftanar Janar Muhammad Bagheri, da matarsa, da 'yarsa (wanda aka gudanar a yammacin ranar Litinin a Husainiyar Fatima al-Zahra), Manjo Janar Sayyid Yahya Safawi, mataimakin Jagoran juyin juya halin Musulunci, kuma babban mai ba da shawara ga babban kwamandan sojojin kasar ya bayyana cewa, Shahidan tsaron kasar Iran sun sadaukar da rayukansu masu tsarki domin fansa ga Kasar Iran ta musulunciu da gwagwarmayar Musulunci a cikin sama da shekaru 40.

Manjo Janar Safawi ya kara da cewa: Al'ummar Iran masu girma sun san 'ya'yansu da kuma masu yi masu hidima da kyau, kuma a cikin 'yan kwanakin nan sun san maha’inta maciya amana karara.

Ina cewa da kwarin gwiwa bisa la'akari da gogewar da na shafe sama da shekaru arba'in na tunkarar makiya, nasara tana ga wannan al'ummar Iran mai girma da karfi, kuma shan kaye shi ne rabon babbar Shaidan da karami.

Ya ci gaba da cewa, “Babban Shaidan da Karamin Shaidan sun kasa cimma burinsu da dabarunsu”. Sun yi kokarin murkushe al'ummar Iran, da raba kasar, da kifar da juyin juya hali. Amma da falalar Allah da tsarewarsa, bisa jagorancin Jagoran Sojojin kasar sun kasa cimma dukkan manufofinsu. Kuma zagayen mutuwar yahudawan sahyoniya ya kara tsananta, kuma an takaita wa'adin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gindaya.

Ya ce: Jinin shahidan da aka zalunta da ba su da kariya a Gaza, Labanon, Siriya, da kuma akidar gwagwarmaya, da kuma shahidai madaukaka na Iran, za su nutsar da gwamnatin sahyoniyawa mai muggan laifuka. Rushewar wannan gwamnati da firaministanta Netanyahu na nan kusa.

Janar Safavi ya gargadi jami'an Amurka, yana mai cewa, "Ya kamata Amurkawa su sani cewa kwangilar “shirin babban yankin gabas ta tsakiya” ya gaza cin ma ruwa.

Ya kara da cewa, a wannan karon, za a kafa sabuwar Gabas ta Tsakiya a kewayen tsarin juyin juya halin Musulunci da kuma kungiyar gwagwarmaya, duniyar Musulunci, wacce ke da musulmi biliyan 1.6, za ta bullo da karfin gaske, kuma mujrima Amurka zata hada yanata yanata.

Ya ci gaba da cewa: Ya kamata kowa ya tabbatar da cewa karfin duniyar musulmi zai zarce na yammacin duniya, wajibi ne yahudawan sahyoniya da Amurka su gane cewa al'ummar Iran ba za su bar su hakan ba. Ba za mu yi watsi da jinin shahidan mu ba, za mu bi su har karshe.

Ya kara da cewa: Mai yiwuwa makiya sun nemi tsagaita bude wuta na wucin gadi, amma mun san su da kyau, kamar yadda muka san muradunsu, da tsarinsu, da sansanoninsu, da dakarunsu a yankin. Ƙarfin IRGC ya zarce Gabas ta Tsakiya. Dubban makamai masu linzami namu suna sete a bankin bayanai da ke hari ga duk sansanonin abokan gaba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin bankin bayanai da sojojin suke da shi, Manjo Janar Safawi ya ce: Makiya suna sane da cewa idan suka sake yin wani kuskure, to dukkanin wurare da sansanonin su za su fuskanci munanan hare-hare a karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci (Allah ya kara tsawaita inuwarsa).

Ya kara da cewa: Sahayoniyawa da Amurkawa ba sa tafiyar da kasarmu da juyin juya halinmu. Tushen wannan tsari ya rataya a wuyan al'ummar Iran abin kauna. Mun sadaukar da shahidai masu yawa tsawon wadannan shekaru, kuma sun karfafa al’umma. Makiya sun nemi yada yanke kauna da bacin rai a tsakanin Iraniyawa, amma halartar jana'izar shahidan da aka zalunta ya nuna irin karfin da al'ummar Iran suke da shi ga duniya.

Manjo Janar Safawi ya jaddada cewa: Al'ummar Palastinu da Lebanon da sauran kasashen musulmi da ake zalunta da kuma al'ummar duniya masu 'yanci a fili sun shaida irin karfin da Iran take da shi, wanda ta ki mika wuya ga Amurka mai mugun hali, ta kuma kai hari kan sansanin Al-Udaid, duk kuwa da cewa makiya sun yi karyar cewa makami mai linzami basu kai ga hadafinsu, amma gaskiyar magana ita ce, akalla makamai masu linzami guda shida ne suka afka wa sansanin.

A karshen jawabin nasa, ya fitar da wani sabon gargadi yana mai cewa: Idan suka fara wani sabon zagaye, to Iran za ta fara wani sabon zagayen da ya wuce dukkan tunaninsu, kuma babbar nasara za ta kasance ta al'ummar Iran abin kauna, kuma kasarmu da albarkar Alkur'ani da Ahlul-Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) ba za a iya yin nasara akanta ba, yayin da shan kashi shi ne makomar Amurka da yahudawan sahyoniya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha